3 Mayu 2020 - 04:59
​ Nijar : Ana Sa Ran Bude Wuraren Ibada Da Makarantu A Ranar 1 Ga Watan Yuni

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa tana tunanin sassauta wasu matakan data dauka na dakile yaduwar cutar corona a cikin kasar ciki har da bude wuraren ibada da makarantu a ranar 1 ga watan Yunin gobe, idan dai har aka ci gaba da samun raguwar masu kamuwa da cutar a kasar.

(ABNA24.com) Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta sanar da cewa tana tunanin sassauta wasu matakan data dauka na dakile yaduwar cutar corona a cikin kasar ciki har da bude wuraren ibada da makarantu a ranar 1 ga watan Yunin gobe, idan dai har aka ci gaba da samun raguwar masu kamuwa da cutar a kasar.

Amma dai gwamnatin kasar ta tsawaita matakan data dauka na dakile yaduwar cutar da makwanni biyu, Kamar yadda ta sanar a taron majalisar ministocinta na mako mako.

A baya bayan nan dai ana ci gaba da samun raguwar masu kamuwa da cutar a alkalumman da hukumomin kiwon lafiya na kasar ke fitarwa.

A ranar 1 ga watan Mayun nan mutum 9 ne aka rawaito cewa sun harbu da cutar a kasar, saidai a karon farko an samu yaduwar cutar zuwa jihohin Agadas da kuma Diffa.

Adadin dai mutanen da suka harbu da cutar a fadin kasar ya kai 728, yayin da kuma wadanda cutar ta yi ajalinsu ya kai 33, sai kuma adadin wadanda suka warke daga cutar ya haura zuwa 478.



/129